A shekara ta 2023, kudurin bayar da ilimi kyauta zai ci gaba da gudana a jihar Kano.
Wannan bayani ya fito daga bakin mai burin yin takarar gwamnan Kano, Alhaji Inuwa Ibrahim Waya, inda ya ce, tsarinsa na tattalin arzikin kasa zai wanzu a kan kudurin ilimi nagartacce ga matasa.
Waya ya yi amana da cewa,jihar Kano ce a kan gaba wajen karfin yawan jama’a idan aka yi la’akari da taswira da tarihin Kano a duniya. Ya ce, tuni tafiya ta yi nisa wajen cim ma matakan gano yadda za a bai wa kowane matashi nagartaccen ilimi a jihar Kano.
Ya ci gaba da cewa, ” a kwanan nan muka kaddamar da rarraba kayan rubutu ga ‘yan firamre da ‘yan sakandare kuma mun rarraba hijabai ga makarantun Islamiyya kuma haka za mu ci gaba da yi har sai mun wadata mabukata a fadin jihar.
Saboda yin na’am da kudirinsa na bunkasa ililmi, Jami’ar Yusuf Maitama Sule Kano ta hannun Tsangayar bunkasa dan- adam ta karrama shi da shaidar yabo saboda hidimta wa dan-adam, musamman a bangaren ilimi kyauta kyauta kuma dole.
An karrama Alhaji Inuwa Ibrahim Waya,a yayin babban taron duniya kan gina dan-adam da jami’ar ta Yusuf Maitama Sule ta shirya.
Majiya Albishi.