Memba a hukumar samar da ingantaccen iri ta Najeriya Ibrahim Musa ya ce ya na ganin rashin bin dabarun noman zamani ne ke kawo tsadar abinci ba batun simoga ba.
Musa a zantawa ta musamman na magana ne kan kalaman ministar kudi Zainab Shamsuna da ke nuna faskawabri ke kawo tsadar shinkafa.
Ibrahim Musa ya ce ba a amfana da binciken da cibiyoyin binciken Najeriya ke yi na bunkasa noma da nau’in iri mai samar da yabanya, hakanan da rashin buda dazuka don noman zamani.
Musa ya ce gwamnati ta bullo da shirye-shirye da dama na bunkasa noma, amma tamkar ba a bin tsarin sau da kafa; don haka ba a ganin ribar hakan a zahiri.
Memban ya kara da cewa ya zama mai muhimmanci Najeriya ta koma 100% noma da kiwo ta hanyar zamani bisa fasahar da cibiyoyin bincike ke fitarwa.