JIRGIN NAJERIYA ZAI FARA AIKI A AFRILUN BADI DUK DA GWAMNATI NA DA KASHI 5% NA JARIN KAMFANIN

Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Hadi Sirika ya ce a na sa ran kamfanin jirgin Najeriya wato “Nigeria Air” zai fara aiki a watan afrilun badi.
Da ya ke magana da manema labaru bayan taron majalisar zartarwa, ministan ya ce gwamnati za ta rike jarin kashi 5% na kamfanin, yayin da sassa masu zaman kan su na Najerita za su rike kashi 46%.


Ministan ya ce sauran kashi 49% zai zama an warewa sassan da ba a ambata ciki har da masu zuba jari na ketare.
Sirika ya bugi kirjin cewa kamfanin zai samar da guraben aiki dubu 70.
A baya dai gwamnati ta yi watsi da kafa kamfanin da nuna ba a shirya yanda zai samu nasara ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram