Mutane sun yi caa su na nuna matukar damuwa ga shirin gwamnatin Najeriya na kara farashin litar fetur.
Shugaban kamfanin fetur NNPC Mele Kyari Kolo ya sanar da niyyar kara farshin da zai cilla litar fetur daga N320 zuwa N340.
Hakan zai boyo bayan janye duk wani rangwame da gwamnati ke sawa don tsaida farashin kan aljihun talaka.
Mutane sun tuno 2012 da ‘yan adawa su ka ce fir ba za su yarda da karin farashin fetur zuwa N97 inda hakan ya bunkasa gagarumar zanga-zanga musamman a Abuja da Lagos.
Daga bisani gwamnatin ta janye N10 ga farashin, litar ta koma N87.
Hawan gwamnatin Buhari ta kara farashi zuwa N145 har ya yi ta karuwa zuwa N165 inda wasu jihohin ma ‘yan kasuwa ke sayar da man ga farashin da ya wuce kima.
Fargabar mutane ba ta wuce yanda za a samu tashin farashin kayan masarufi da rashin bayani mai gamsarwa na dalilan da ‘yan adawa su ka marawa zanga-zanga baya a zamanin gwamnatin da ta shude.