An Janye Dokar Katse Layukan Waya Saboda Matsalar Tsaro A Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da ɗage dokar katse hanyoyin sadarwar da ta kafa a watan Oktoba na shekarar nan da mu ke ciki saboda matsalar tsaro da jahar ta ke fuskanta

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan a ranar Juma’ar nan

Aruwan ya ce, tuni Gwamnatin Jihar ta umarci kamfanonin sadarwa da su dawo da hanyoyin sadarwar da aka riga aka katse a baya.

Jahar Kaduna na daga cikin jahohin da ke fuskantar matsalar rashin tsaron a jahohin Arewa maso yamma na Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram