Ana sa ran a ɗauki tsawon shekara 1 kafin a kammala aikin gadojin ƙasa 2 a katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da kwangilar gina manyan gadojin kasa guda 2 a cikin birnin Katsina.

Gadojin wadanda za a gina a Kofar Kaura da Kofar Kwaya za su lakume zunzurutun kudi har naira biliyan 5.8 kuma kamfanin TRIACTA ne aka baiwa kwangilar aikin.

A sa’ilin da yake kaddamar da soma aikin a Kofar Kaura, Gwamna Aminu Masari ya ce gadojin idan aka kammala su, za su amfani masu ababen hawa da ke shiga da fita birnin Katsina, musamman ta fuskar rage cunkoso.

Masari ya kara da cewa, samar da manyan hanyoyin ruwa a Katsina da Malumfashi da Jibia da Funtua wanda ya lakume sama da naira biliyan 15 wani bangare ne na kudurin gwamnatinsa tun daga lokacin da ta karbi mulki na daga darajar manyan garuruwan jihar.

Tun da farko, a nasa jawabin, Kwamishinan ayyuka da gidaje da sufuri, Tasi’u Dandagoro, ya jinjina wa gwamnatin Masari bisa na kammala ayyukan hanyoyin da ta gada daga gwamnatin Shema na kimanin naira biliyan 7 da doriya tare da soma wasu sabbi guda 19 da gyara wasu 17 gami da gina hanyoyin karkara na kusan naira biliyan 3.

Kwamishinan ya kuma yaba da yadda gwamnatin ta tallafa tare da sake fasalin hukumar sufurin jihar, KTSTA, ta sama mata sabbin motoci 25 wanda ya bata damar tsaya da gindinta ta fuskar biyan albashin ma’aikatanta da sayen karin motoci.

Shugaban kamfanin da zai gudanar da aikin, Sadek Auwal da babban jami’in tuntuba a kan aikin, Engr. Sama’ila Bawa sun bayar da tabbacin yin aiki mai inganci tare da kammala shi a kan lokacin da aka tsara na watanni 12.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram