Najeriya ta kammala shirinta na ƙaddamar da jirgin ruwa na yaƙi da sojojinta na ruwa suka ƙera.
Wannan dai shi ne karo na 3 da rundunar ta ƙera jirgin yaƙi a cikin gida.
Aikin ƙera jirgin, ya samu jagorancin
Injiniyoyin rundunar
bisa kulawar kamfanin Navy Dockyard Limited, mallakin rundunar da ke unguwar Victoria Island a Jihar Legas.
An bayyana cewa jirgin zai taimaka wajen yaƙin da ake yi da ƴan fashin teku a gaɓar ruwa sassa daban-daban na ƙasar nan.