Shugaba Buhari ya ba jami’an tsaro umarnin su fatattaki ƴan bindigar da ke hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari na ya ba manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin su fatattaki ƴan bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja da ma na sauran sassan ƙasar.

BBC ta ce, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ministan harkokin cikin gida na ƙasar Rauf Aregbesola ne yasanar da hakan a ranar Alhamis ɗin nan bayan taron majalisar tsaro ta tarayya wanda shugaban ƙasar ya jagoranta a fadarsa.

Ya bayyana cewa shugaban ya ba dukkannin jami’an tsaron ƙasar umarni da kada su yi ƙasa a gwiwa su tabbatar sun kawar da duk wasu ƴan fashin daji da masu garkuwa da mutane da duk wasu nau’uka na laifuka.

Hanyar Abuja zuwa Kaduna dai ta zama tamkar tarkon mutuwa ganin yadda ake yawan samun ƴan bindigan na yi wa matafiya kwantar ɓauna.

Ko a makon nan sai da ƴan bindigan suka sace gwamman mutane da kuma kashe wani fitaccen ɗan siyasa a Najeriyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram