Yadda Na Taimaka Wajen Hana Tazarcen Obasanjo – Thabo Mbeki

Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Thabo Mbeki ya bayyana cewa, shi da tsohon shugaban Najeriya, Janar Abdussalamu Abubakar sun hada kai wajen dakile aniyar tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ta zarcewa da mulki bayan karewar wa’adinsa a shekarar 2007.

Idan dai za a iya tunawa, yunkurin tazarcen Obasanjo ya samu cikas ne daga majalisar dattawa a karkashin jagorancin Sanata Ken Nnamani.

A sa’alin da yake magana ta yanar gizo a lokacin wani taro a Abuja a ranar Alhamis, Mbeki ya yi bayani a kan irin rawar da ya taka tare da Janar Abubakar wajen dagewa domin ganin gyaran tsarin mulki a zamanin mulkin Obasanjo bai yiwu ba.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Mbeki na cewa, bayan kiran da ya yi wa Obasanjo ta waya domin bayyana damuwarsa a kan yunkurin, sai kuma shi da Janar Abubakar suka amince su shiga cikin batun domin hana yi wa kundin tsarin mulkin garambawul wanda idan aka yi shi zai bai wa Obasanjon damar dorawa a kan kayyadadden wa’adinsa na shekara 8.

Mbeki wanda shi ne shugaban Afirka ta Kudu na biyu bayan mulkin mallaka, ya jinjina wa Janar Abdussalam Abubakar bisa kokarin da ya yi wajen kare dimokuradiyya a shekarar 2006 ta hanyar dakile kudurin Obasanjo na yi wa tsarin mulkin kasar karan tsaye a wancan lokaci, shekaru kusan 7 bayan mika mulkin ga Obasanjo din.

Ya kara da cewa wannan turka-turka ta sanya ya fahimci irin namijin kokari da karfin fada-a-jin da Janar Abdussalam ke da shi wajen kare dimokuradiyya da tabbatar da zaman lafiya da hadin kan Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram