Ƙasar Tailan Na Shirin Dakatar Da Matafiya Daga Ƙasashen Afirika 8 Shiga Ƙasar Saboda Ɓullar Sabuwar Cutar Korona

Gwamnatin ƙasar Tailan a ranar Assabar ɗin nan
ta shelanta cewa zata dakatar da matafiya ma su zuwa ƙasar daga ƙasashen Afirika 8 waɗan da aka samu ɓullar sabuwar cutar Korona.

Hukumar lafiya ta duniya watau WHO, ta ba sabuwar cutar suna Omicron kuma masana na kan ƙoƙarin fahimtar sabuwar koronar da kuma gano ko akwai yiwuwar sake ma allurar rigakafin korona tsari.

 

Hoto: Lillian Suwanrumpha / AFP

Kafar sadarwar Channels ta ce sabon nau’in korona ɗin har ya shiga ƙasashen yankin Asia da wasu ƙasashen waje.

Sashen kula da cututtuka na ƙasar ta Tailan ya ce mutanen da suka fito daga ƙasashen Botswana da Eswatini da Lesotho da Malawi da Mozambique da Namibia da South Africa da Zimbabwe za ta hana su shigar ƙasar daga watan Disamba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram