Ƙungiyar yan sa kai a arewa maso gabashin Najeriya ta kashe ƴan Boko Haram uku da kama ɗaya a yayin da ƴan Boko Haram ɗin suka je satar amfanin gona a kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

BBC ta ce Kafar PRNigeria ta ruwaito cewa ƴan Boko Haram sun kai hari ga wasu manoma tare da satar amfanin gonarsu inda ƴan sa kan suka yi bata-ka-shi da su.
Wani wanda ya gane ma idonsa lamarin ya ce mayaƙan sun kashe manoma biyu da kuma raunata wani mutum guda.