Ƴan bindiga sun yi garkuwa da DPO a jihar Edo

Rahotanni daga jihar Edo a Najeriya na cewa an yi garkuwa da wani DPO a jihar.

Kafar PRNigeria ta ruwaito cewa an sace ɗan sandan mai suna CSP Ibrahim Aliyu Ishaq wanda shi ne DPO na ofishin ƴan sanda da ke Fugar, a kan hanyar Auchi zuwa Agenebode a jihar Edo.

Kafin a kai CSP Ishaq jihar Edo a kwanakin baya, ya taɓa aiki a ofishin ƴan sanda da ke Dakata a jihar Kano.

A bana dai an kai hare-hare ga ofisoshin ƴan sandan Najeriya da dama musamman a kudancin Najeriya inda aka ƙona ofisoshinsu da ƙwace makamansu.

#BBC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram