Hukumar Lafiya Ta Duniya watau, WHO, ta bayyana sabon nau’in cutar korona a matsayin wani “abin damuwa” ta kuma raɗa masa suna da Omicron.
BBC ta ruwaito cewa Sabon nau’in cutar yana sauyawa da sauri, sannan bayanan da suka fara fitowa a game da shi sun nuna cewa akwai hatsarin karuwar sake kamuwa da shi.

Ranar 24 ga watan Nuwamba ne karon farko da aka bayyana wa WHO bullarsa daga afirka Ta Kudu, kuma an gano ya fara bulla a Botswana da Belgium da Hong Kong da isra’ila.
Ƙasashe da dama sun yanke shawarar taƙaitawa ko ma hana zuwa cikinsu daga Kudanci Afirka.
Jami’ai sun ce a a hana jiragen da suka fito daga Afirka Ta Kudu, Botswana, Zimbabwe, Namibia, Lesotho, Eswatini, Mozambique da Malawi daga shiga Birtaniya.