Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya buƙaci ƴan ƙasar da su rinƙa bin dokokin hanya kuma su daina keta dokar kan hanyoyin ƙasar .
Wannan na fitowa ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Boade Akinola, ya fitar inda ya ambato Shugaba Buhari yana mai bayyana hakan ranar Juma’a yayin ƙaddamar da titi mai tsawon kilomita 304 wanda ya tashi daga Sokoto-Tambuwal-Kontagora-Makera.
Shugaban kasar, wanda Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya wakilta, ya ce gwamnatinsa ta duƙufa wajen yin ayyuka da ta dauki alƙawura lokacin yaƙin neman zabe, wadanda suka haɗa da gina hanyoyi masu kyawu..
BBC ta ce, Sanarwar ta ambato Shugaba Buhari yana jero dokokin da mutane suke karyawa wadanda suka hada da dora kayan da suka wuce kima a kan motoci, zubar da fetur da dangoginsa a kan tituna da kuma mayar da gefen tituna a matsayin wurin ajiye motoci na dindindin.