FUDMA Ta Sanya Ma Ɗakin Kwanan Ɗalibai Mata Sunan Uwar Gidan Gwamna Masari.

Jami’ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma a jahar Katsina, FUDMA, ta sanya ma wani gini na ɗakin kwanan ɗalibai mata da ke mazauninta na din-din-din sunan matar gwamnan jahar, Hadiza Aminu Masari.

Shugaban Jami’ar Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi ya bayyana dalilin sanya ma ɗakin kwanan ɗaliban sunanta inda ya ce saboda gudunmawar da ta ke bayarwa ga bunƙasa ilimin ƴaƴa mata a faɗin jahar.

Hadiza Masari da ta ke jawabi ta yaba ma jami’ar dangane da ƙoƙarin da ta ke wajen yaye nagartattun ɗalibai da suke da hazaƙa, ta kuma shawarci shugabannin jami’ar da su ci gaba da wannan namijin ƙoƙari da su ke.

Uwar gidan gwamnan ta nuna jin daɗinta bisa karamcin da aka yi mata na lakaɗa sunata ga ɗakin kwanan ɗaliban sannan ta ƙara da janyo hankalin ɗaliban jami’ar gaba ɗayansu da su guji faɗawa cikin harkokin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi domin samun ingantattar rayuwa.

Daga ƙarshe shugaban jami’a tare da rakiyar sauran malaman makarantar da kuma waɗan da suka rufa ma uwar gidan gwamnan baya suka zagaya domin nuna mata bangarorin ɗakunan kwanan ɗaliban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram