Tsohon shugaban Ƙasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya buƙaci ƴan ƙasar su rungumi tabi’ar amfani da makamashi wanda ba ya gurbata muhalli domin a samu ƙasa mai tsafa.
Obasanjo ya yi kiran ne ranar Juma’a nan a yayin da yake ƙaddamar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin 2MW a ɗakin Karatun da ya gina da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.
BBC ta ce, Jaridar ThisDay ta ambato tsohon shugaban ƙasar yana cewa amfani da makamashi mai aiki da hasken rana “yana da arha kuma yana da kyau ga muhalli.”