Abdulsalami Ya Ce Salon Sasanci Da Yin Sulhu Ya Kamata Shugabanni Su Ɗauka Wajen Magance Rikice-Rikice.

Tsohon shugaban Ƙasar Najeriya, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, ya ce dole ne ƙasashen Afirka su canja salon da suke amfani da shi wajen wanzar da zaman lafiya yana mai cewa amfani da ƙarfin soji ba zai kawo lumana ba.

Ya bayyana haka ne a Abuja ranar Asabar ɗin nan a wani taro da aka gudanar domin karrama shi.

Abubakar ya ce har yanzu nahiyar Afirka na fama da rikice-rikice “iri daban-daban,” wadanda ya ce suna ciki manyan ƙalubalen da ke addabar nahiyar.

BBC ta ce, Jaridar ThisDay, wadda ta ambato shi yana wadannan kalamai ta ce tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci shugabannin Afirka su rungumi “sasantawa da yin sulhu” wajen magance rikici-rikice.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram