Gwamnan Jihar Borno da ke Arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce an bankaɗo sunan jarirai a jerin wadanda ake biya albashi daga lalitar Jihar.
Gwamnan ya ce an gano sunayen ne a Karamar Hukumar Shani ta Jihar, bayan aikin tantance ma’aikata a Jihar.
Wannan lamari ya sanya zargin cewa wasu jami’an gwamnati ne ke wawure albashi da sunan ma’aikatan bogin da ake da su a fadin Jihar.
Gwamna Zulum ya bayyana hakan ne yayin bikin al’adu na Menwara a garin Shani, ranar Asabar.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Zulum ya ce maƙasudin ƙirƙiro shirin tantance ma’aikatan domin gano na bogi daga cikinsu, amma masu adawa da hakan a Ƙaramar Hukumar suka shirya zanga-zangar rashin nuna goyon baya.
Ya ce, “Ina sanar da ku cewa bayan kammala tantancewar, mun bankaɗo sunayen jarirai a jerin ma’aikata, yayin da muka kuma gano cewa a duk wata, akan kashe Naira miliyan 19 wajen biyan ma’aikatan bogi a kowanne wata a Karamar Hukumar Shani.
“Akwai iyali ɗaya da muka gano sunan ma’aikatan bogi 300. Ina fargabar in hakan ya ci gaba, akwai yiwuwar Karamar Hukumar ta gaza biyan albashi a nan gaba kaɗan,” inji Gwamnan.
Ya kuma yi zargin cewa guraben ayyukan da ya kamata a ba mutanen Karamar Hukumar ana sayar wa wasu akan N250,000, lamarin da ya ce yana hana matasan da suka yi karatu samun aiki.