Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce ranar Talata nan mai zuwa za a bude layukan wayar salula a fadin jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin zaɓen shugabannin jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ranar Asabar ɗinnan.
In za a iya tunawa dai a farkon watan Satumba ne aka katse layukan a wani mataki na daƙile hare-haren ƴan bindiga da masu satar mutane.
Sai dai a kwanakin baya an bude layukan wayar salula da intanet da aka katse a Gusau, babban birnin jihar.
Matawalle ya kara da cewa za a sake buɗe kasuwannin da aka rufe sakamakon matsalar tsaro.
“Bayanan da muka samu sun nuna cewa an samu raguwar matsalolin tsaro a yankunan jihar nan, kuma nan da Litinin ko Talata za mu sake bude layukan wayoyin salula, kowa da kowa zai samu damar yin waya,” in ji gwamnan.
#BBC