Mataimaki shugaban gamayyar ƙungiyoyin mutanen Arewacin Najeriya na shiyyar Arewa maso Yamma, Jamilu Charanchi ya baiyana damuwarsa game da dokokin da gwamnatin jahar Katsina ta sanya da nufin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar jahar.
Charanchi, ya ce dokar ba ta haifar da komai ba sai halin ƙunci da ta sanya al’umma musamman masu ƙaramin ƙarfi sun fi kowa galabaita da shiga halin ha’ula’i.
Ya ce tun da aka sanya dokar ba a ji an ce yau ga ƴan ta’adda sun fito daidai lokacin da dokar babura ke fara aiki an kama su ba.
Charanchi wanda ya buga misalin da hare-haren da aka kai a yankin Batsari da kuma ƙauyen Barawa, ya ce ƴan ta’adda sun kai hare-haren ne a daidai lokacin da ya kamata a ce dokar ta fara aiki ko ma sun fara ta’addancin kafin lokacin amma har su gama abinda su ke su tafi ba tare da an kama su ba.
“Abin damuwa ne da tausayi kwarai idan ka je kasuwannin da gwamnati ta hana sayar da dabbobi ka ga yanda mutanen da ke wannan sana’ar suka koma mabarata da halin maula.” in ji shi.
Don haka ya ce duk mutumin da ya ce dokar ta haifar da ɗa mai ido to wannan mutumin kodai ba garin ya ke ba ko kuma ya faɗi son zuciyarshi.
Idan za a iya tuwa dai a kwanakin baya ne gwamnatin jahar ta fito ta ce ta samu nasarori dangane da kafa dokar.