Masari Ya Ce Matasa Sun Zama Raggwaye Sun Tsaya Jiran Gwamnati Ta Ba Su Aikin Yi.

Gwamna Aminu Masari na jahar Katsina ya ƙalubalanci matasa da su tashi tsaye wajen ganin sun dogara da kansu.

Gwamna Masari ya faɗi haka ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata a yayin ƙaddamar da soma aikin gadojin ƙasa guda biyu da gwamnatinsa zata yi a ƙofar ƙaura da ƙofar kwaya a cikin birni katsina, inda ya ce samun ayyukan dogaro da kai ga matasa shine hanya mafi sauƙi wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar jahar.

Saidai Masari ya ce maimakon matasa su tashi tsaye su nemi na kansu sai suka ƙi hakan suka tsaya jiran gwamnati ta basu aikin albashi.

Masari na ganin cewa idan har matasa za su dage da yin ayyukan da za su dogara da kansu to za a shawo kan matsalar tsaro, ya ƙara da cewa matsalar tsaro ta kowa da kowa ce don haka kowa ya ɗaukin matakan kare kanshi.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta haɗa hannu da kowa wajen ganin an samu ayyukan yi da samun zaman lafiya a faɗin jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram