Mutune 14 ne su ka rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota da ya afku a Jihar Jigawa da yammacin Lahadi nan
Hadarin dai ya faru a lokacin da matafiyan ke kan hanyarsu ta zuwa garin Karkarna a Ƙaramar hukumar Ƴankwashi.
Kafar sadrwa ta Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa Waɗanda lamarin ya faru a idonsu sun shaida mata cewa wuta ta tashi a sa’ilin da motoci kirar Golf guda biyu su ka yi arangama da juna.
A cewarsu, ba’a samu ceto ko mutum guda ba saboda yadda wuta ta kama bayan haɗarin.