Hukumar ɗakile cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutane 110 da suka kamu da cutar korona a Najeriya.
Alƙalumman sun nuna mutum 27 suka kamu da cutar a jihar Imo sai a jihar Katsina da aka samu mutum 23 a ranar Lahadi.
A jihar Rivers an samu mutum 20, sai jihar Ondo mai mutum 11. A Kaduna ƙarin mutum tara suka kamu da cutar.
Yanzu jimillar mutum 214,092 cutar ta shafa a Najeriya amma 207,254 sun warke yayin da cutar ta kashe mutum 2,976 a Najeriya.
#BBC