Gwamnatin jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya ta ce daga ranar 1 ga watan Disamba ma’aikatan jihar za su dinga yin aikin kwana huɗu a mako.
Matakin da gwamnatin ta ɗauka zai ba ma’aikatan jahar damar yin aikin kwana ɗaya daga gida, domin inganta aiki da ba su damar samun lokaci ga iyalinsu da kuma samun lokacin noma.
BBC Hausa ta ce, sanarwar ta ce matakin na daga cikin darussan da aka koya lokacin annobar korona da ke buƙatar samun lokacin samun annashawa saɓanin tsohon tsarin da aka saba da shi na aiki.
Hakazalika sanarwar ta kuma ce lokacin aiki zai koma daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma daga Litinin zuwa Juma’a.
Dukkanin ma’aikatan jihar baya ga makarantu da ma’aikatan lafiya za su yi aiki ne daga gida a ranar Juma’a.