Fursunoni 262 sun Cika Rigunansu Da Iska Sun tsere daga gidan yarin Jos.

Hukumomi a Najeriya sun ce fursunoni 262 sun tsere daga gidan yarin Jos, babban birnin jihar Filato da ke arewacin kasar.

BBC Hausa ta ce, Wata sanarwa da hukumar kula da gyaran hali ta kasar ta fitar ranar Litinin ɗin nan ta ce fursunoni tara sun mutu yayin da ma’aikacin gidan yarin daya ya rasu, kana aka kashe dan bindiga daya yayin harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a kurkukun ranar Lahadin da ta gabata

Hukumomi sun ce maharan sun buɗe wuta sannan suka ci karfin masu gadin gidan yarin kafin su fasa inda fursunonin suke.

an sake kama fursunoni goma da suka tsere, yayin da har yanzu ake neman 252.

Babu taƙamaiman tabbaci game da ainihin ‘yan bindigar da suka kai harin da kuma dalilinsu na yin hakan.

Tun da farko, hukumomin sun ce an ritsa da maharan a cikin gidan yarin, amma daga bisani sun ce sun tsere bayan kuɓutar da daruruwan fursunoni tate da kashe fursuna tara da ma’aikaci ɗaya.

Shi dai gidan yarin yana kusa da hedikwatocin hukumomin tsaron ƙasar da ke birnin na Jos – waɗanda suka haɗa da hedikwatar Ƴan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram