Kwastan a Katsina Sun Kama Kaya Da Harajinsu Ya Kai Sama Da Milyan 176

hukumar kwastan a Katsina ta kama kayyakin da darajar harajinsu ta kai sama da Naira Milyan 176 a cikin wata ɗaya.

Shugaban hukumar na jahar, Ɗalha Wada Cheɗi ne ya sanar da haka a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a shelkwatar hukumar da ke Katsina, a ranar Litinin ɗinnan.

Wada Cheɗi ya ce daga farkon wannan watan na Nuwanba zuwa 29 hukumar ta kama kayayyakin da harajinsu su ya kai milyan 176,453,850 na naira.

Cheɗi ya sanar da cewa daga cikin kayan akwai maganin mai ɗauke da sinadarin ƙarfi jiki da hana jiki ya gaji, Diclofenac wanda shi kaɗai harajinshi ya kai naira milyan 5, sai kuma zunzurutun kuɗi har naira bilyan 71,35000 da suka kama wani mutum yana ƙoƴarin haurawa da su ƙasar Niger.

Hakazalika shugaban ya ce sun kama tabar wiwi wadda aka taho da ita daga jahar Lagos zuwa Katsina.

Sauran kayayyakin sun haɗa da buhunan ahinkafa da na aya da katon-katon na taliya da makaroni da man girki da motoci da wasu manyan wuƙaƙe ma su hatsarin gaske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram