Mutane 7 ciki har da yaro ɗan shekara uku ne suka mutu, wasu uku na kwance a asibiti a yankin Pemba na Zanzibar, bayan cin naman kunkuru mai ɗauke da guba.
Cin naman kunkuru dai ba wani baƙon al’amari ba ne a Zanzibar musamman ga mazauna tsuburai da waɗanda ke zaune a yankunan gaɓar teku.
Sai dai a halin yanzu, hukumomi sun haramta cin naman.
A kan samu kunkurun da namansa kan gurɓata sakamon cin wani abu mai ɗauke da guba.
Kawo yanzu dai, babu tabbacin wacce irin guba ce a naman knkurun da ta janyo mutuwar mutanen, kamar yadda ƙungiyar Turtle Foundation charity ta Zanzibar ta bayyana.
Akalla iyalai biyar ne suka ci naman kunkurun a yankin Pemba da ke fitaccen tsuburin Zanzibar a ranar Alhamis, kamar yadda shugaban ‘yan sandan yankin Juma Said Hamis ya shaidawa BBC.