An kama tabar wiwi ta sama da naira milyan 18 da aka taho da ita daga Lagos zuwa Katsina.

Jami’an hukumar Kwastan a Katsina sun ce sun kama wasu mutane biyu a cikin mota ɗauke da tabar wiwi wadda kuɗinta suka kai darajar naira milyan 18 sun taho da ita daga Lagos za su kawo Katsina.

Shugaban hukumar a Katsina, Ɗalha Wada Cheɗi ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai da hukumar ta ke yi duk ƙarshen kowane wata wanda ta yi a ranar Litinin ɗinnan.

Cheɗi ya ce hukumarsa ta hannanta tabar wiwin da masu laifin ga hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA, ta ƙasa reshen jahar Katsina domin tsananta bincike.

Hukumar NDLEA dai ta sha gaɗa cewa ƴan ta’adda na amfani da migun ƙwayoyi wajen aikata ta’addanci a jahar ta Katsina da ma sauran jahohin da ke fuskantar matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram