Ana fargabar rashin tabbacin aikin rigakafi ga sabon nau’in cutar korona na Omicron.

Shugaban kamfanin magunguna na Moderna a Amurka ya yi gargaɗin cewa rigakafin da ake amfani da su yanzu na cutar korona da wuya idan za su iya yin tasiri a kan nau’in Omicron na cutar, inda ya ce rigakafin ba za su yi aiki kamar yadda suka yi tasirin a kan nau’in Delta ba.

Majiyar jakadiya BBC Hausa, ta ce, Stephane Bancel ya shaida wa Financial Times cewa ba a tantance iya yadda zai iya aiki ba

Saidai abin da masana kimiyyar da ya tuntuba ke cewa shi ne labarin ba mai daɗi ba ne.

Yanzu haka dai ƙasashe 10 na yankin tarayyar Turai ne aka samu 42 waɗanda suka kamu da nau’in cutar Omicron kamar yadda hukumar yaki da cutuka ta yankin ta faɗa.

Shugaban hukumar Andrea Ammon, ta ce ana kuma duba wasu mutum shida da ake zargin cewa su ma suna ɗauke da sabon nau’in cutar.

Yanzu haka dai manyan kamfanonin haɗa rigakafin korona uku sun ce za su ga yadda za su inganta rigakafin domin aiki a kan sabon nau’in cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram