Gwamna Tambuwal Na Sokoto Ya Haramta Ayyukan Ƴan Sa-kai AFaɗin Jahar

Gwamnatin Sokoto ta haramta ayyukan ƴan sa-kai a faɗin jihar tare da inganta aikin ƴan banga.

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal wanda ya sanar da ɗaukar matakin a ranar Litinin a wani taron tsaro na jihar, ya ce sha’anin yan sa-kai shi ya ƙara haifar da matsala a Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

Ya ce ƴan sa kai suna yin gaban kansu ba tare da bin doka da oda ba. “Ba za mu ci gaba da ƙyalewa ba domin mun san illar hakan.”

“Mun fito da doka da ta haramta ƴan sa-kai kuma duk wanda ke son taimakawa jami’an tsaro, to ya shiga aikin banga,” in ji gwamna Tambuwal.

BBC Hausa ta ce Sanarwar da ofishin gwamnan ya fitar ta ce duk wanda aka kama zai sha ɗaurin shekara 14 ko biyan tara ta naira 500,000.

Dokar ta kuma ce duk wanda aka kama da makami a jihar zai sha ɗaurin shekara bakwai a gidan yari ko ya biya tarar naira 200,000.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ɗauki matakin ne domin magance matsalolin tsaro da ke damun jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram