Babbar Kotun Gwamnatin Taryya da ke Abuja ta bayyana cewa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai iya zuwa Kano a duk lokacin da ya ga dama, kuma korarsa daga Jihar da gwamnati ta yi take haƙƙinsa ne da ’yancin rawar gaban hantsi.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, Kotun, ta kuma umarci Gwamnatin Jihar Kano da Babban Sufeton Ƴan Sanda da Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya (SSS) da su biya shi tarar Naira miliyan 10, sannan su ba shi hakuri a cikin akalla jaridu guda biyu.