Shari’o’i 3 Da Ganduje ya Sha Kaye.

Mutane na ta faman tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta dangane da shari’o’i 3 da Gwamna Abdullahi Ganduje na jahar Kano da ke Arewacin Najeriya ya sha kaye.

Hakan na zuwa ne bayan hukuncin kotun tarayya a Abuja da ta yi a ranar Talatar nan inda ta umarci Gwamnan da ya nemi afuwar tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II wanda ya sauke ba bisa ƙa’ida ba.

Hakazalika kuma duk dai a ranar ne kotu ta rushe shugabannin jam’iyyar APC na jahar waɗanda ke ɓangaren Ganduje inda ta ba ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau nasara.

Shari’o’i ukun da Gwamnan ya sha kaye a ɗan tsakanin nan sun haɗa da, hukuncin kotu tsakaninsa da ɗan jarida Ja’afar Ja’afar bisa ga badaƙalar wani faifan bidiyo da shi Ja’afar Ja’afar ɗin ya saki wanda aka nuno Gwamna Ganduje na ƙarɓar dalolin ƙudi daga wani da ake zaton ɗan gwangila ne ke bashi na goro.

Kotu ta ba Ganduje umarnin ya biya Ja’afar Ja’afar Naira Dubu 800,000,00 bisa ɓata mashi lokaci da yayi bayan da shi Gwamnan da kanshi ya ce ya janye shari’ar.

 


Na biyu kuma Sarki Sunusi II, inda kotu ta ce ya biya shi naira milyan 10 ya kuma bashi haƙuri.

 

Na uku kotu ta rushe shugabannin APC ɓangaren Gandujen ta bai wa ɓangaren shekarau inda Dan Zago Ya Zama Shugaban Jam’iyyar na jahar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram