Alaramma Ahmad Sulaiman ya zama kwamishinan Ganduje

Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano ya naɗa Alaramma Ahmed Sulaiman kwamishinan ilimi na biyu a jihar Kano.

Majiyar Jakadiya ta BBC Hausa ta ruwaito cewa, malam Ahmad Sulaiman ne ya tabbatar da ba shi wannan muƙamin a saƙon da ya wallafa a shafinsa na Facebook yana mai godiya ga gwamnan.

A cikin hotunan nasa da ya wallafa yana tare da gwamnan, a gefe akwai Sheikh Abdullahi Balalau wanda shi ne shugaban Ƙungiyar Izala, da kuma sakataren ƙungiyar na ƙasa Sheikh Kabir Gombe.

Alaramma Ahmad Sulaiman ya roƙi Allah ya sa albarka a kujerar da ya samu da kuma roƙon addu’ar jama’a kan taya sa riƙo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram