Hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta Jahar Kaduma wato SUBEB ta ce zata kori malaman makaranta 233 tare da miƙa su kotu a hukunta su saboda amfani da satifiket na bogi.
Wannan na fitowa ne a yayin wani taron manema labarai da hukumar ta shirya ƙarƙashin jagorancin Tijjani Abdullahi don sanar da irin nasarorin da ta samu dangane da ƙoƙarin da ta ke na inganta ilimi a makarantun gwamnati da ke faɗin jahar, wanda gwamnan ya ɗora a shafinsa na Facebook.
Hukumar ta ce bisa ga nauyin da ya rataya kanta na ta tabbatar da cewa duka malaman da suka gabatar da satifiket din na su sun cancanta don haka sai ta duƙufa wajen tantance satifiket ɗin domin tabbatar da sahihancinsu wanda ta yi a cikin watan Afrilu na shekarar 2021.
Saidai hukamar ta ce bayan aikin tantancewar wanda shine ƙa’idar da mutum zai tsallake kafin ɗaukarsa aikin, inda ta tantance mutane 451 ta hanyar tuntuɓar makarantun da malaman suka ce sun yi karatu kuma ta ce makarantu 9 a ciki 13 da ta tuntuɓa sun bada amsa.
Bisa ga amsoshin da hukumar ta samu daga makarantu, ta gano cewa malamai 233 sun yi amfani ɗa satifiket na jabu inda makaranta ɗaya kaɗai ta kalubalanci sahihanci satifiket 212 da aka yi amfani da su a matsayin na ta.
Don haka hukumar ta sha alwashin korar malaman tare da iza keyarsu kotu don su fuskanci hukunci.
Hakazalika hukumar ta yi alkawarin dora sunayensu a saman kafafen sadarwar zamani domin kowa ya gani.