Kotu ta bada umarnin a ba shugaban IPOB Nnamdi Kanu damar rawar gaban hantsi.

Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta ba hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), umarni da ta tabbatar da shugaban ƙungiyar ƴan a-waren Biafra Nnamdi Kanu ya samu ‘cikakkiyar walwala’ yayin da yake tsare a hannunsu.

Wannan umurni ya biyo bayan ƙorafin da lauyoyinsa suka yi na cewa wanda suke karewa an hana shi walwala ko canza kaya da yin addininsa ba ya iya wa a yayin da yake tsare.

Sauraren shari’ar gaggawar da aka yi ya zo bayan tsegwamin da lauyoyinsa suka yi cewa ɗage shari’ar da aka yi tun da farko ya saɓawa sauraren shari’ar cikin hanzari da aka shirya yi wa shugaban na IPOB.

Kanu wanda ake tuhuma da cin amanar ƙasa bai halarci zaman kotun ba a ranar Alhamis. An ɗage shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2022.

#BBC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram