Motar bunburutu ɗauke da man fetur ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus a Katsina

Daga Umar Usman

Wata motar da ake zargin ana sana’ar bunburutu da ita ta kama da wuta ta ƙone ƙurmus a Unguwar Malali da ke Katsina.

Motar ƙirar Golf 1 mai lamba AE755KNA wadda aka ce ta ɗauko man fetur da yammacin ranar Litinin ɗinnan ta kama da wuta ne a daidai lokacin da ma su ita ke ƙoƙarin zuge man da ke cikin tankin

Waɗanda lamarin ya faru a gaban idonsu sun ce motar ta fara ci da wutar ne tun misalin ƙarfe 6 na yamma kuma kafin ma’aikatan hukumar kashe gobaraba da gudunmuwar jama’a su kashe ta sai da ta sha mota biyu ta ruwa.

Ba a samu asarar rai ko raunata wani ba saidai wutar ta ƙona bangon makwancin masu motar,tareda ƙone wayar wutan lantarki dake wajen.

A halin yanzu dai jami’an ƴan sanda sun tafi da konannar motar, yayinda maigidan da kuma direban motar sukayi batan dabo.

Akwanakin naya ne gwamnatin jahar ta sanya dokar hana sana’ar man fetur ɗin a cikin dokokin da ta sanya da nufin shawo kan matsalar tsaro da ke addabar jahar.

Maiunguwar yankin, Muɗɗaha Abubakar, ya ce sun jima suna faɗakarwa tareda jan hankulan jama’a kan illar wannan sana’a musamman a cikin unguwa, inda ya shawarci al’ummar unguwar da sukai rahoton duk wani da suka ga yana irin wannan Sana’a domin ɗaukar mataki akansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram