Za a ɗauki ƴan banga aikin samar da tsaro a makarantun Abuja

Hukumomi a babban birnin Tarayya Abuja na Najeriya sun bayyana cewa suna shirin ɗaukar ƴan banga domin gadin makarantu saboda barazanar tsaro da ake fuskanta a Abujar.

BBC Hausa ta ce Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, daraktan gudanarwa a ɓangaren tsaro na hukumar birnin na Abuja yana cewa an riga an kammala shirin ɗaukar ƴan banga da za su tabbatar da tsaron makarantu a faɗin yankin .

Wannan dai ya biyo bayan wasu rahotanni na tsaro da ke cewa ƴan bindiga daga jihohin da ke makwabtaka da Abuja suna tsallakowa zuwa cikin birnin na Tarayya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram