Ƙasar Najeriya na buƙatar ta ci gaba da zama a matsayinta na ƙasa ɗaya – Taron NPC

Shugaban Ƙungiyar Nigerian Peace Corps Dr. Mustapha Abubakar ya ce Ƴan Najeriya dole ne su rungumi al’adar zama da juna ba tare da nuna banbance-banbance ba a tsakaninsu.

Mustapha ya faɗi haka ne a yayin taron gangamin wayar da kan matasa na yini uku da ƙungiyar ta shirya a Abuja dangane da sake nanata buƙatar da ke akwai wajen ganin an rungumi juna ba tare da la’akari da banbacin da ke tsakanin al’umma ba kamar yadda shugabannin baya suka yi.

Shugaban ya ce mutane ne suka haɗa kansu suka bunƙasa ƙasar nan wadda mu ke morarta a yanzu inda ya buga misali da irinsu Tafawa Balewa da Sardauna da Nnamdi Azikiwe da Abiola ya ce sun zo ne daga wurare daban-daban amma kuma suka haɗa kansu suka maida ƙasar ta zama ƙasa ɗaya domim amfanin kowa da kowa saboda haka babu dalilinda za mu ce mu raba kawunanmu a yau.

Shima a nasa bayanin Jakadan wanzar da zaman lafiya na majalisar ɗinki duniya Ambasada Hussaini Coomassie cewa yayi ya kamata wasu daga cikin malamai su sauya salon yadda su ke kallon sha’anin aikace-aikacen ƴan ta’adda.

Ambasada Commassie ya ce duk malamin da ya samu dama ya iya zuwa wurin ƴan ta’adda to kamata ya yi ya yi masu wa’azi su daina kashe mutane amma ba ya rinka nuna cewa ba su da laifi ba kamar yadda wasu malan ke rajin haka a Najeriya.

Daga ƙarshe Kwamandan rundunar ƙungiyar na Katsina Ashiru Bala Ƴanɗaki ya bayyana irin yadda ire-iren waɗan nan tarukan da ke ƙoƙarin haɗa kan ƙasa a wuri ɗaya suke da muhimmaci a halin da ake ciki a yanzu.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron sun hada da matasa da manyan jami’an gwamnati da masu riƙe da masarautun gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram