Masari na fatan wanda zai gaje shi ya gina ma Mani da Mashi Matatar ruwa da zata samar masu da ruwan sha

Gwamna Masari Ya Ce Yana Fatan Wanda Zai Gajeshi Zai Yi Ƙoƙari Yayi Matatar Ruwa Da Zata Samar Da Ruwan Sha A Ƙananan Hukumomin Mani Da Mashi.

Gwamnatin jahar Katsina ƙarƙashin jagoranci Aminu Masari ta ce tana kan ƙoƙarin dawo da madatsar ruwa ta dam ɗin Ajiwa kamar yanda aka gina ta tsawon shekaru 40 da suka wuce.

Gwamna Masari ne ya faɗi haka a yayin da ya kai ziyarar duba yadda yanayin aikin ke tafiya a dam ɗin a ranar Juma’ar nan, inda ya ce aikin wanda ake akai yanzu zai laƙume kuɗi har milyan ɗari 942

Masari ya ce injinan da ke wurin waɗanda sun kwashe tsawon shekaru 40 duk sun gaji sun lalace shi yasa ba a samun ruwa yadda ya kamata don haka bayan gama gyaran dam ɗin kashi na farko sai sake wata matatar ruwa wadda ya ke fata idan gwamnatin da zata gaje shi ta zo zata yi amfani ta gina matatar da za ta ba mutanen ƙananan hukumomin Mani da Mashi ruwa.

“Ɗan sanina ƙalilan baka da hanyar da zaka kai ruwa Mani daga nan indai ba ta hanyar ruwan dam ba domin ƙasar dai dutse ne ba ka samun wani wadataccen ruwa” in ji shi.

Masari ya kuma bada tabbacin cewa nan da watan 5 na shekara mai zuwa duk ayyukan da su ke kai na runwan zasu yi iya ƙoƴarinsu su ga sun gama su.

Gwamnan ya ƙara da cewa ana hasashen dam ɗin zai rinka samar da ruwa aƙalla lita milyan 50 bayan an kammala aikin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram