Kwamatin da ke yaƙi da cutar korona a Najeriya ya amince a fara jaddada wa ƴan ƙasar rigakafin cutar da aka yi musu a farko
Dr Faisal Shu’aibu wanda shine Shugaban hukumar lafiya a matakin farko ne ya bayyana haka a ranar Juma’ar nan inda yake cewa an ɗauki matakin ne da haɗin gwiwar Ma’aikatar Lafiya da zummar tsaurara yaƙi da cutar.
Majiyar Jakdiya ta naƙalto cewa BBC Hausa ta ce shugaban ya ce za a yi wa mutanen da tuni suka yi rigakafin sau biyu na samfurin AstraZeneca ko Moderna ko Pfizer Bio-N-Tech ko kuma waɗanda aka yi wa samfurin Johnson and Johnson sau ɗaya.
Sharaɗin da aka shimfiɗa na samun allurar shi ne sai mutum ya kai shekara 18 da haihuwa ko fiye, sannan sai mutum ya yi wata shida da yin allura ta biyu ta samfurin AstraZeneca ko Moderna ko Pfizer Bio-N-Tech, ko kuma tsawon wata biyu da yin Johnson and Johnson.
Za a fara gudanar da allurar ce daga ranar 10 ga watan Disamba a dukkan jihohin Najeriya.