Ganin yanda zaɓen shekara ta 2023 ke ƙara ƙaratowa a Najeria, shugaban ƙungiyar nan ta matasa masu rajin goyon bayan tsohon shugaban ƙasar Atiku Abubakar, Hon. Bello Mu’azu yayi kira ga matasan Najeriya da su kuji barin gurɓatattatun ƴan siyasa na amfani da su.
Ya ce matasa su daina bari ana amfani da su wajen gurɓata ƙasar tare da tada zaune tsaye wajen ganin an kawo naƙasu inda ya ce wasu ne daga cikin ƴan siyasa da ba su buƙatar ci gaba da kuma ɗorewar demokiraɗiyya a ƙasar musamman a game da zaɓe mai zuwa.
Mu’azu yayi wannan furuci ne a yayin da yake magana da ƴan jarida jim kaɗan bayan ƙaddamar da shugabannin ƙungiya na Katsina a ranar Lahadin nan.
Ya ce kowa ya sani cewa duk lokacin da aka ce zaɓe ya zo to ƴan siyasa suna ba matasa kuɗi naira 1000 ko 500 wani lokacin ma har ɗari 2 ake ba su da kuma yin alƙawurra da ba su cikawa.
Kamar faɗa, cewa akwai milyoyin matasa a ƙasar waɗanda suke da shaidar kammala Digiri da NCE amma ba su da aikin yi shin su matasa ba su da dama ne a ƙasar ko ba su ne shugabannin gobe ba? inji shi.
Mu’azu ya ƙara da cewa Atiku Abubakar ne kaɗai ke da duk cancantar da ake buƙata kuma shi zai magance duk matsalolin da ke addabar Najeriya indai har aka ba shi dama a zaɓen 2023.