Wani jami’in gwamnati a Jamhuriyar Nijar ya ce wasu ƴan ta’adda sun kashe sojoji 12 a wani artabu da aka yi a kudu maso yammacin ƙasar.
BBC Hausa ta ruwaito cewa, Jami’an tsaron sun fuskanci mummunan hari daga ɗaruruwan mayaƙa a kusa da kauyen Funio ranar Asabar.
Sai dai jam’in gwamnatin ya ce an samu nasarar kashe ƴan ta’adda da dama.
Ana alaƙanta hare-haren na baya-bayan nan a yankin Sahel da ke yammacin Afrika kan mayaƙa masu alaƙa da kungiyar IS wadda ke iƙirarin jihadi.