Canjin Naira 50 yayi Sanadin Rasa Rayuwar Wani Mai Sayar Da Sigari

Rundunar Yan sanda a Jihar Ogun sun damƙe wani matashi da ya yi ma wani mai sayar da sigari dukan mutuwa, wanda ya yi ajalinsa a dalilin canjin Naira 50.

Mahaifin mamaci Adamu Abubakar shi ne ya shigar da ƙara aka kuma cafke matashin da ke zaune a yankin Oladun a Ikotun na Jihar Legas.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, Dan sanda mai shigar da kara, ya shaida wa kotu cewa matashin ya zo shagon ɗan nasa Mika’ilu Adamu da ke unguwar Ajegunle a Idiroko don sayen sigari.

inda ya ci gaba da cewa matashin ya dawo daga baya don karbar canjinsa na Naira 50 a wajen ɗan nasa.

A cewarsa, lamarin ya kai su ga cece-kuce, har ta kai ga matashin ya hau ɗansa da duka.

Abubakar ya ci gaba da cewa, a nan take ɗan nasa ya yanke jiki ya faɗi, wanda hakan yasa suka garzaya da shi asibiti inda a can ne aka tabbatar da mutuwarsa

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi ya ce bayan samun rahoton faruwar lamarin, an aika da jami’an ƴan sanda sun kuma yi nasarar cafke wanda ake zargin da silar rayuwar mai sayar da sigarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram