Rundunar ƴan sandan jahar Katsina ta yi nasarar cafke wane matashi mai suna Yusuf Abdullahi wanda rundunar ta ce yana cikin ƴan ta’addan da suka kashe hakimin Ƴantumaki a ƙaramar hukumar Ɗanmusan jahar Katsina
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ne ya gabatar da matashin ga manema labarai a hedikwatar ƴan sanda da ke Katsina a ranar Talatar nan.
SP Isha ya ce kama matashin ya biyo bayan tsananta bincike da ƴan sandan suka yi tun daga ranar da ƴan ta’addan suka je gari na Ƴantumaki suka kashe hakimin garin Alh. Abubakar Atiku tare da mai gadinsa mai suna Gambo Isah.
Ya ce a ranar ɗaya ga watan Yuni na shekarar 2020 ƴan ta’addan suka je garin suka yi wannan aika aika kuma a yanzu ga ɗaya daga cikinsu sun kama
Ɗan ta’addan Yusuf Abdullahi wanda ya ce shekarunsa ashirin da haihuwa kuma ɗan asalin ƙauyen Kagara ne da ke ƙaramar hukumar Matazu, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi har ya faɗi sunayen wasu mutum huɗu da ya ce tare da su suka yi ta’addanci.
Muatne huɗun da ya ce tare da su suka yi kisan kan sun haɗa da Shamsu da Ibrahim da Salmanu da Kabir kuma har yanzu suka cikin daji a laɓe.