Ɗan sanda Ya Bindige Kansa Bayan Ya Kashe Mutane 6 Ciki Harda Matsarshi.

Wani ɗan sanda a kasar Kenya ya bindige mutane shida har lahira, ciki har da matarsa, tare da jikkata wasu biyu sannan daga bisani ya harbe kansa da bindiga.

Lamarin dai tuni ya haifar da zanga-zanga inda fusatattun mazauna yankin marasa galihu a birnin Nairobi suka rufe hanya da ƙona tayoyi.

A yayin da ƴan sanda suka gudanar da binciken sun gano cewar, jami’in nasu ya fara harbin matarsa a wuya da bindiga kirar AK-47, kafin ya buɗewa sauran jama’ar dake kusa wuta, nan take kuma ya kashe mutane 6 kafin ya kashe kansa.

RFI ta ruwaito cewa, ɓangaren waɗanda suka jikkata kuma, yanzu haka an kwantar da wasu mutane biyu a asibiti.

Har yanzu dai ba a kai ga tantance dalilin da ya sa ɗan sandan ya tafka wannan ta’asa ba, amma wata majiya ta ce jami’in da matarsa sun daɗe suna samun rashin fahimtar juna.

Wannnan lamari dai ba baƙo ba ne ba domin ba shi ne karo na farko da ake samon jami’an tsaro a Kenya suna halaka abokan zamansu ba.

Ƙo a watan da ya gabata, wani jami’in ɗan sanda ya buɗe wuta kan abokan aikinsa a tsakiyar ƙasar ta Kenya, inda ya harbe ɗaya a kai kafin ya gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram