Jami’an Tsaro Sun damƙe Wani Uba Da Ke kwana Da ƴar cikinsa A Ogun

Rundunar Jami’an tsaron farin kaya Sibul Difens NSCDC a jihar Ogun ta cafke wani magidanci mai suna Rojaiye Balogun dake da shekaru 65 da laifin yi wa ƴarsa ƴar shekaru 17 fyaɗe.

Jaridar Premiumtimes Hausa ta ruwaito cewa Shugaban rundunar Kolawole Taiwo ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis ɗin nan inda ya ce sun samu labarin wannan ɗanyen aiki da Balogun yake yi daga wajen kawun yarinyar wanda ya shigar da ƙara a ofishinsu.

Shuganan ya ce da jin wannan labari ba tare da ɓata lokaci ba rundunar ta hanzarta damƙo Balogun a ƙauyen Imomo dake Ijebu-Ode.

Ya ce bayan sun zo ofishinsu da Balogun ya ce yarinyar agolar gidansa ce ba shine ainihin mahaifin ta ba.

Ya ci gaba da cewa mahaifiyar yarinyar ce matarsa kuma ta kawo yarinyar gidansa ne tun tana ƴar shekara 10 bayan sun yi aure.

“Tsohon wanda ya nuna ya yi nadamar abin da ya aikata ya ce sau ɗaya ya taba yin lalata da yarinyar kuma shima dai sharrin shaiɗan ne a cewarsa.

Saidai ita yarinyar ta ce Balogun ya daɗe yana lalata da ita kuma maganar da ya faɗi ya ce shi ba mahaifinta ba ne ƙarya yake yi shine ainihin mahaifinta.

Yarinyar ta ce har naira 1, 000 ɗaya ya taɓa yi mata alƙawarin bata amma da ta ƙi bashi haɗin kai sai ya danne ta da ƙarfin tsiya ya biya buƙatarsa a ranar.

Ta kuma ce tuni ta daɗe da sanar da mahaifiyarta abin da ke faruwa tsakaninta da mahaifin na ta amma mahaifiyar ta ƙi yarda da zancenta.

Daga ƙarshe shugaban rundunar NSCDC, Taiwo, ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike idan ta kammala za ta kai Balogun kotu domin yi masa hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram