Shugaba Mohammed Bazoum na Jamhuriyar ya bayyana cewa ba ƙaramin kuskure aka yi ba wajen gaza daƙile safarar makaman da ake yi daga ƙasar Libya waɗanda ƴan ta’adda ke amfani da su wajen kai hare hare a Yankin Sahel.
Bazoum ya bayyana cewa Ƙasashen Sahel na buƙatar taimako daga sauran ƙasashe na duniya ta fuskar tattara bayanan sirri da jiragen yaƙi tare da horar da jami’an tsaro domin tinkarar babbar matsalar tsaron da ke addabi yankin.
Bisa ga lamarin tattara bayanan sirri shugaban na Nijar yace babban matsalar ita ce rashin sanya hannu daga abokan aikin su wajen yaƙi da safarar makaman dake fitowa daga Libya, wanda ya ce shine babban dalilin rura wutar hare haren ƴan ta’adda
Kamar yadda IFR Hausa ta ce, Shugaban ya ce ƙungiyoyin ƴan ta’addan dake kai hare hare a yankin Sahel ɗin sun banbanta sakamakon kazaman makaman da suke ɗauke da su, waɗanda suke samu cikin sauƙi daga masu safarar su daga kasar Libya.
Bazoum yace wani lokaci ya kan yi tunanin irin makaman da ƴan ta’adda ke ɗauke da waɗanda suka zarce na sojoji, musamman ganin irin samfurin makaman harbo makamin roka da ake kira RPG da kuma bindigogi masu sarrafa kan su da ake kira M80 da suka mallaka.
Tun daga shekarar 2011 lokacin da aka kashe shugaban Libya Muammar Ghadafi ƙasar ta faɗa cikin ruɗani da tashin hankali da kuma rikicin ƙabilancin wanda wani lokaci ƙasashen ketare ke rura wutar sa.