Za A Yi Bikin Nuna Fina-Finai Na Duniya A Ƙasar Saudiyya

Bayan ɗage haramcin nuna fina-finai kimanin shekaru 4 a Saudiyya za a buɗe bikin fina-finan na farko a birnin Jeddah na ƙasar.

Bikin zai gudana ne na tsawon kwanaki 10 inda za a nuna fina-finai138 daga sassa daban daban na duniya.

BBC Hausa ta ce, za a karrama darakta mace ta farko a Saudiyya Haifa al-Mansour – wacce ta fara fim din Wadjda da ta lashe kyauta.

Manufar bikin ita ce haɓɓaka masana’antar fina-finai a ƙasar Saudiyya ta fuskar shirya fina-finai da kuma kasuwarsu da nunawa a sinima da aka buɗe tun shekarar 2018.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram