EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Hafsoshin Soji A Gaban Kotu

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya, EFCC, ta maka tsohon babban hafsan rundunar sojin kasar, Laftana Janar Kenneth Minimah a gaban kotu bisa zargin karkatar da kudaden sayen makamai har naira biliyan 13.

Sauran wadanda aka gurfanar tare da Minimah a gaban wata babbar kotun Abuja, sun hada da tsohon shugaban sashen kasafin kudi, Manjo Janar A. Adetayo da kuma tsohon daraktan kudi na rundunar, Birgediya Janar R. Odi.

A cikin karar da hukumar ta EFCC ta gabatar, ta ce, a ranar 15 ga watan Agusta, 2016, ta karbi wani rahoton kwamitin binciken yadda aka kashe kudaden sayen makaman askarawan kasar (CADEP), daga shekarar 2007 zuwa 2015, a karkashin shugabancin AVM John Ode mai ritaya.

Ta ce rahoton, ya yi zargin cewa, a tsakanin shekarar 2010 da 2015, rundunar sojin Najeriya ta karbi dubban miliyoyin naira daga hannun gwamnatin tarayya domin sayen makamai amma sai aka gano cewa, a maimakon hakan, wasu manyan jami’an sojin kasar ne suka yi gaban kansu suka karkatar da akalar kudaden.

Hukumar ta EFCC ta fada ma kotun cewa, an cire kudaden daga asusun rundunar sojin sannan aka tura su zuwa asusan wasu kamfanonin da ba su da wata alaka da rundunar.

A sabili da wannan tuhuma, hukumar ta ce, ta rubuta wa rundunar sojin kasar takardar bukatar jami’an sojin 3 su mika kansu domin gurfanar da su a gaban kotun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram