Ganduje Ya Ce A Makaranta Ya Karanta Siyasa Ba A Bakin Titi Ya Tsince Ta Ba

Gwamnan jahar Kano da ke Arewacin Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya ce su siyasarsu a makaranta suka karance ta ba a bakin titi suka tsince ta ba.

Gwamnan na magana ne a cikin wata muryarsa da RFI ta naɗa a yayin wata fira da ta yi da gwamnan.

Ganduje ya ce samun rarrabuwar kai a siyasa ba sabon abu ba ne domin kuwa ko an samu rabuwar kan kuma ana zowa a daidaita.

“Mu yan siyasa ne mun san wani lokaci za a ɓata wani lokaci kuma a shiraya, amma mu abinda mu ke cewa wannan siyasa ba wai mun tsince ta a bakin titi ba ne mun shige ta ne fiye da shekara 40 da suka shige kuma bugu da ƙari ma ita muka karanta a jami’a kuma ita mu ke yi” in ji shi.

Ya ce saboda haka sun san cewa maganar siyasa magana ce ta haƙuri sannan kuma ɗan siyasa ba ya da abokin gaba na didindin sai ma dai amini na dindindin kamar yadda ya faɗa

Gwamnan ya ƙara da cewa maganar rikinsu na jam’iyya da suke fuskanta a jahar uwar ƙungiya ta ƙasa ta jam’iyyar APC ta shiga cikin lamari kuma yana saran za a samu fahimtar juna tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram